6 Mayu 2026 - 17:56
Source: ABNA24
Hizbullahi Na Ci Gaba Da Ruwan Makamai Akan Wuraren Isra'ila

Hizbullahi Na Ci Gaba Da Ruwan Makamai Akan Wuraren Isra'ila

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rahotonnin fage na nuna cewa Hizbullah ta lalata tankar Isra'ila a garin Al-Bayadah da makami mai linzami a yau, kuma makamin ya kai hari kai tsaye kan wurin da aka nufa. Sannan Hizbullah ta kuma sanar da cewa sun harba makamai masu linzami kan taron sojojin Isra'ila da motocinsu a kusa da Khalat Al-Raj a garin Deir Ezzor, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsu.

Sannan bayan Hizbullah ta harbo wani jirgin helkwafta sojojin Isra'ila sun tabbatar da harin makami mai linzamin na Hizbullah kan jirgin helikwaftan. wanda Kakakin rundunar sojin Isra'ila ya sanar da cewa an harba makami mai linzami daga sama zuwa sama kan jirgin helikwafta na rundunar gwamnatin Isra'ila a kudancin Lebanon. Wanda Hizbullah ta sanar da cewa ta kai hari kan jirgin helikwafta na rundunar Isra'ila a sararin samaniyar garin Al-Bayadah a kudancin Lebanon da makami mai linzami daga sama zuwa sama kuma ta same shi.

Your Comment

You are replying to: .
captcha